Isa ga babban shafi
Faransa

Jam’iyyar Hollande da kawayenta sun lashe zagayen farko na zaben ‘Yan Majalisa

Kwarya-Kwaryan Sakamakon zaben ‘Yan Majalisu a Faransa ya nuna Jam’iyyar Gurguzu ta shugaba Francois Hollande, da kawayenta, na shirin karbe jagorancin Majalisar kasar, sakamakon nasarar da suka samu a zaben da aka gudanar a karshen mako. Hakan ke nuna Hollande zai samu damar aiwatar da kudirorin gwamnatinsa saboda samun rinjayen kujerun majalisa.

Katin Jefa kuri'ar zabe a Faransa
Katin Jefa kuri'ar zabe a Faransa REUTERS/Jean-Paul Pelissier
Talla

Jam’iyar tare da abokan tafiyarta, sun samu kimanin kashi 47 na kuriun da aka kada, yayin da Jam’iyar UMP ta Tsohon shugaban kasa, Nicolas Sarkozy, ta samu kashi 34.

Masu sa ido game da Siyasar Faransa , sun yi hasashen, Jam’iyar Hollande da kawayenta zata lashe tsakanin kujeru 283 zuwa 329 daga cikin kujeru 577 na Majalisar kasa, dan samun rinjaye.

A zaben ‘Yan Majalisu na bana an samu kasa da kashi 60 na wadanda suka fito kada kuri’a sabanin zaben ‘Yan Majalisu da aka gudanar a shekarar 2007.

Sama da ‘Yan takarar 6,500 suke neman kujerun Majalisar 577. Kuma kashi 40 cikinsu Mata ne. Akwai dai kujeru 11 da aka ware wa Baransawa mazauna kasashen waje.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.