Isa ga babban shafi
EU-Jamus

Jamus ta ki amincewa da sabon tsarin ceto euro

Kungiyar Tarayyar Turai, za ta duba yiyuwar amincewa da dokar samun karfin saka hannunta ga tsarin kasafin kudin kasashenta domin kaucewa matsalar tattalin arziki da ta shafi wasu daga ciki. Amma wannan na zuwa ne bayan gwamnatin Jamus ta ki amincewa da wani sabon tsarin ceto euro.

Shugabar gwamnatin Jamus Chancellor Angela Merkel a lokacin da take zantawa da manema labarai a birnin Berlin
Shugabar gwamnatin Jamus Chancellor Angela Merkel a lokacin da take zantawa da manema labarai a birnin Berlin REUTERS/Fabrizio Bensch
Talla

A wani rubutaccen rahoton hukumar gudanarwa ta kungiyar tarayyar Turai, ya nuna cewa hukumar tana da ikon sake zayyana kasafin kudin kowace kasa daga cikin kasashenta, tare da gabatar da shawarar yin kuri’a ga sauran kasashen kungiyar kamin zartaswa.

Akwai dai bukatar Shugaban kasar Faransa François Hollande, da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, su cim ma matsaya dangane da wannan shirin, kasancewar sun gudanar da taron tattaunawa na musamman kan batun bashin kasashe masu amfani da kudin Euro tsakaninsu.

Amma kuma Angela Merkel ta bukaci dorewa kan matakan tsuke bakin aljihu domin gurgunta matsalar bashi, sai dai shugaba François Hollande ya nuna bukatar sake duba manufofi, da matakan magance tattalin arzikin kasashensu.

Tun a jiya, shugabannin manyan kasashen 4 masu karfin tattalin arziki da suka hada da Faransa, da Jamus da Italiya, da Spain, sun gudanar da wani taro inda suka tattauna kan wannan matsalar kafin taron kasashen baki daya.

Amma kuma matsalar da ake samu ita ce ta takon saka tsakanin kasar Jamus da Faransa wadanda ya zama wajibi su amince da wannan bukatar kamin a zartas.

Taron kasashen na zuwa ne a dai dai lokacin da Kamfanin Moody ya rage darajar wasu bankunan kasasr Spain 27.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.