Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta rage kudin harajin Man fetir

Firaministan Faransa Jean-Marc Ayrault ya yi alkawarin rage kudin harajin man fetur da gas, na wani dan lokaci kafin gudanar da shirin din din da zai samar da daidaito ga farashin mai.

Prime Ministan Faranasa Jean-Marc Ayrault yayin da yake jawabi a gaban 'yan majalisar Faransa
Prime Ministan Faranasa Jean-Marc Ayrault yayin da yake jawabi a gaban 'yan majalisar Faransa REUTERS/Vincent Kessler
Talla

Tun a yakin neman zaben shi, shugaban Faransa Francois Hollande ya yi alkawarin dakatar da hauhawar Faranshin mai.

Sai dai saukar da farashin mai ya yi a kasuwannin duniya, ya sa gwamnatin Hollande aiwatar da shirin. Amma a ‘yan makonnin nan farashin ya hau a kasuwannin duniya, lamarin da ya sa masu amfani da shi a cikin gida ke ji a jikinsu, a daidai lokacin da tattalin arzikin Farasa ya tsaya cik.

Amma kamfanonin Mai a Faransa sun gargadi gwamnatin kan zaftare farashin mai, inda suke cewa wannan matakin zai sa a sami karancin shi.

Firaminista Jean-Marc Ayrault yace a ranar 28 ga wannan watan Augusta, ministan kudi Pierre Moscovici zai gana da kamfanonin mai, da kungiyoyi masu zaman kan su, don samar da hanyar da za a aiwatar da shirin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.