Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta fi korar bakin haure a 2012

Wani Rahoto da aka fitar ya nuna cewa Adadin bakin hauren da aka kora daga kasar Faransa, a cikin shekara ta 2012,  shi ne adadi mafi yawa da aka samu a kasar a cikin shekarun da suka gabata.

Bakin haure a Arizona da ake kora a Guatemala
Bakin haure a Arizona da ake kora a Guatemala © Getty Images / John Moore
Talla

Wata majiya a kasar ta Faransa ta ce mutane 32, 822 ne aka kora daga kasar saboda rashin takardun da ke ba su iznin zama kasar, sabanin mutane 32, 912 da aka kora a shekarar a 2012. Kuma wannan yasa aka samu yawan adadin wadanda zuwa kashi 11.9 idan aka kwatanta da 2011.

Batun korar bakin haure yana daga cikin manyan alkawullan da tsohon shugaba Sarkozy ya yi a lokacin yakin neman zaben shi domin samun goyoyn bayan Faransawa.

Wasu na hannun damar Ministan harkokin cikin gidan kasar Manuel Valls, sun bayyana karuwar wadanda aka kora a 2012, abu ne da ya samo asali daga umurnin da bangaren shari’a na kasar ya bayar mai halatta korar wadanda ba su da cikakkun takardu zaman kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.