Isa ga babban shafi
Fransa

Faransawan da aka 'yantar a Kamaru sun isa birnin Paris

Faransawan nan 7 da aka sace sannan kuma aka yi garkuwa da su a kasar Kamaru kafin a sake su, a yau asabar sun isa birnin Paris na kasar Fransa inda suka gana da sauran ‘yan uwansu.

Iyalan Moulin-Fournier tare da shugaba François Hollande a filin jirgin sama na d'Orly
Iyalan Moulin-Fournier tare da shugaba François Hollande a filin jirgin sama na d'Orly AFP PHOTO/KENZO TRIBOUILLARD
Talla

Shugaban kasar ne wato Francois Hollande da kansa ya tarbe su a filin saukar jiragen sama na Orly da ke birnin Paris, kwana guda bayan sakinsu daga garkuwar da aka yi da su ta tsawon watanni biyu a wani wuri, inda kuma ake dora alhakin yin garkuwa da su a wuyan kungiyar Boko Haram da ke arewacin Nigeria.

A cewar shugaba Hollande, Faransa ce baki daya ke cikin farin ciki da murna sakamakon ‘yantar da wadannan mutane, inda ya kara da cewa gwamnatinsa ba ta biyya diyya domin ‘yantar da wadannan mutane ba, to sai dai sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar a jiya juma’a. ta yi godiya ga hukumomin kasashen Najeriya da kuma Kamaru dangane da irin rawar da suka taka wajen ‘yantar da mutanen wadanda aka sace a ranar 19 ga watan Fabarairun da ya wuce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.