Muna da matsalar inda za mu ajiye bakin hauren da aka ceto a ruwa - Italiya
Yara kanana da dama aka ceto daga cikin bakin haure 163 da jirgin ruwansu ya samu matsala, a mashigin ruwan Sicily dake kasar Italiya. Bayanai sun nuna cewar, bakin hauren sun fit one daga kasahsen Masar da Syria, inda suka kunshi yara 66 da mata 45.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Amakon da ya gabata, Ministar harkokin wajen kasar Italiya, Emma Bonino ta koka da yadda bakin haure ke shiga kasar ta Italiya.
“Mu samu kanmua a cikin wani mawaycin hali, domin bamu da isasshen wurin da zamu ajiye su.” In ji Magajiyar garin Portopalo di Capo, Michele Taccone.
Ta kuma kara da cewa a yanzu haka mutane suna zaune a wasu rumfunan tenti guda biyu inda aka sama musu wajen ba haya guda takwasa kacal.
Ceto bakin haure a ruwan shine lamari na baya bayan nan da ya auku a yankin, inda a ranar Asabar din da ta gabata wasu mutane bakwai suka mutu saboda basu iya ruwa ba.
Yake yake da matsalar talauci a wasu yankunan Asiya da Afrika na daga cikin dalilan da kansa bakin hauren ke neman mafaka a kasashen Turai kamar yadda rahotanni ke nunawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu