Hollande zai sha kaye a zaben 2017-bincike
A wani binciken jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a kasar Faransa, sakamakon binciken yace kashi hudu cikin Biyar na Faransawa sun yi imanin Francois Hollande zai sha kaye a zaben 2017 saboda matsalolin tattalin arziki da suka shafi rashin aikin yi da karin kudaden haraji.
Wallafawa ranar:
Hollande mai ra’ayin Gurguzu wanda ya kada Sarkozy a zaben shugaban kasa da ya gabata yana fuskantar suka saboda tabarbarewar magance matsalar rashin aikin yi a kasar.
Binciken jin ra’ayin Jama’ar da kafafofin yada labaran Le Figaro da kafar Telebijin ta LCP suka gudanar, sakamakon yace kashi 76 cikin 100 sun bayyana Hollande a matsayin wanda ya saba alkawali, kuma kashi 68 sun ce yana da rauni wajen tafiyar da gwamnati.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu