Isa ga babban shafi
Faransa

Sabon shirin farfado da tattalin arziki Faransa

Gwamnatin faransa na shirin magance barazanar boren da take samu, hatta ma daga Jam’iyyar Socialist mai mulkin kasar akan matakan da take dauka domin cike gibin da kasar ta sama a fannin tattalin arzikinta.Firaministan kasar Manuel Valls wanda ya sha fama da matsin lamba akan batun rage kashe kudi wajen yiwa jama’a aiki da gwamnatin sa ta kuduri aniyar yi, da akalla Euro Billiyan 50 kwatankwacin Dollar Amurka billiyan 69 a cikin shekaru 3 masu zuwa, ya lissafa wasu jerin shirye shiryen sassautawa akan kudurinsu na farko.

Manuel Valls,  Firaministan Faransa
Manuel Valls, Firaministan Faransa REUTERS/Charles Platiau
Talla

Firaministan kasar dake samun taimakon shugaban kasa Francois Hollande, Valls ya gabatarwa Majalisa bukatun rage dawainiya domin kasar ta cimma shirin cike gibin tattalin arzikin ta,
Amma yanda aka kudurin gudanar da aikin, ya dausashe shirin samarwa jama’a kayan more rayuwa, abinda ya harzuka mutane hattama a jam’iyyar Socialist mai mulkin kasar.

Wasu ‘yan majalisa ma sun dauri aniyar kalubalantar Valls akan kasawarsa ta dorewa da biyan bukatun al’umma, inda kememen da ‘yan majalisu 40 daga bangaren Socialist suka yi ya muzanta Gwamnatin kasar ta Faransa,
A dai wajen Valls ya sanar da daukar matakan daidaita al’amura.
Ba’a dai tabbatar da ko nawa wannan shirin yin gyaran zai twatsa ba, amma Valls ya ce, zai tabbatar sun maida euro billiyan 50 da aka datsiye daga 2015 zuwa 2017 masu zuwa lokacin da Hollande zai kammala wa’adin mulkin sa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.