Rikici ya barke a kudancin Ukraine
Rikici ya barke a garin Odessa da ke kudancin Ukraine tsakanin ‘Yan sanda da dubban mutanen kasar da ke kishin Rasha, a yayin da gwamnati ke zargin Rasha da kokarin tarwatsa Ukraine.
Wallafawa ranar:
‘Yan sanda sun yi arangama ne da dubban mutanen Ukraine da ke kishin Rasha, kuma an samu hasarar rayukan mutane da dama.
Kusan wannan arangama a garin Odessa, ta bude wani sabon babin rikici ne, a daidai lokacin da hukumomin Ukraine ke kokarin dakile tarzomar da ta addabi gabacin kasar.
Ganin haka ne kuma yasa Fira Minista Arseniy Yatsenyuk, ya zargi Rasha da yunkuri ruguza kasar Ukraine bayan ta amince da Crimea da suka amince su koma ikon Rasha.
Masana siyasa a Turai sun bayyana fargaba akan Ukraine na dab da fadawa yakin basasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu