Isa ga babban shafi
Bosnia

Asarar rayuka sanadiyyar ambaliyar ruwa a kasar Bosnia

Ambaliyar ruwa da ta afka wa kasar Bosnia ta yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 14, yayin da aka kwashe wasu fiye da dubu 15 daga yankunan da lamarin ya shafa.

Ambaliya a birnin Budapest na Romania
Ambaliya a birnin Budapest na Romania (©Reuters)
Talla

Rahotanni sun ce ana ci gaba da samun saukar ruwan sama mai karfinn gaske, wanda ya haddasa cikar koguna da koramu musamman ma a yankin arewacin kasar.

Hukumomi sun ce ambaliyar da aka sama a bana, ita ce mafi muni da ta taba faruwa a kasar a cikin wannan karni na 21.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.