Isa ga babban shafi
Faransa

An fara binciken akwatin nadar bayan jirgin Algeria

Kwararri sun fara gudanar da bincike akan bakin akwatin nadar bayanan jirgin saman kasar Algeria da ya yi hadari cikin makon jiya lokacin da yake keta sararin samaniyar kasar Mali.

Bakin akwatin jirgin Algeria
Bakin akwatin jirgin Algeria
Talla

A ranar litinin da ta gabata ne aka isa da bakin akwatin a kasar Faransa, inda jami’an cibiyar gudanar da binciken ta BEA suka fara nasu aiki a wannan talata.

To sai dai wata majiya ta bayyana cewa akwai yiyuwar akwatin ya yi matukar lalacewa bayan fadowar jirgin, kuma idan hakan ta tabbata, zai kasance abu mai wuya a iya samun bayanan da ake bukata daga gare shi.

Shi dai wannan jirgi ya fado ne a wani yanki da ke cikin Mali, bayan ya taso daga Ouagadougou zuwa birnin Alger dauke da mutane 116 mafi yawansu Faransawa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.