Isa ga babban shafi
Faransa

Binciken bacewar hodar iblis a hannun 'yan sandan Faransa

Hukumomi a kasar Faransa, a wannan litinin sun kaddamar da bincike domin gano wata hodar ibilis mai nauyin kilogram 50 wadda ta bata a hannun ‘yan sandan birnin Paris.

Hodar Iblis da jami'an tsaron Faransa suka kama
Hodar Iblis da jami'an tsaron Faransa suka kama REUTERS/Tyrone Siu
Talla

Wannan Hodar ibilis da aka kiyasta cewa za ta kai ta milyoyin kudadin Euro, ta bata ne a lokacin da take hannun jami’an hukumar ‘yan sanda mai fada da manyan laifufuka da ke birnin Paris, lamarin da ya yi matukar janyo hankulan hukukomin tsaron kasar har ma suka kaddamar da bincike da nufin gano wadanda suka yi awun gaba da ita.

A cewar Hukumomin matukar dai aka gano cewa akwai ganganci ko kuma sabawa doka a game da bacewar wannan hoda, to lalle kuwa za a aiwatar da hukuncin mai tsanani akan wadanda ke da hannu a lamarin.

An dai kama wannan hodar ibilis ne a cikin watan yulin da ya gabata, kuma an bayar da ajiyarta ne a wani sashe da ke da matakan tsaro na ma’aikatar ‘yan sandan, amma da aka bukaci sake duba halin da wannan ajiya ke ciki a ranar 23 ga watan jiya, sai aka tarar cewa ba ita ba duriyarta.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da hodar Ibilis ke bacewa a hannun ‘yan sandan Faransa ba, yayin da ko cikin watan Afrilin da ya gabata ma an cafke wasu ‘yan sanda 4 da ke aiki da wannan sashe, bayan da wata mata ‘yar kasar Canada ta yi zargin cewa sun yi mata fyade a lokacin da take tsare a hannunsu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.