Isa ga babban shafi
Ukraine-Rasha

Ukraine ta kange motocin kayan jinkai daga Russia

Hukumomin kasar Ukraine sun ci gaba da tsare ayarin motocin da Rasha ta tura dauke da kayayyakin jinkai, a daidai lokacin da mazauna birnin Doneskt da sojojin na Ukraine suka yi wa kawanya ke a cikin hali na bukata.

Ayarin motoci dauke da kayan jinkai daga Rasha zuwa Donestk
Ayarin motoci dauke da kayan jinkai daga Rasha zuwa Donestk REUTERS/Maxim Shemetov
Talla

Yanzu haka dai motoci 300 makare da kayan abinci, magunguna da dai sauransu, Ukraine ta hana wa shiga yanki har sai an gudanar da bincike kan wadannan motoci.

Ko a wannan asabar dai sojojin Ukraine sun sanar da lalata wasu tankokin yakin kasar Rasha da ‘yan tawaye ke amfani da su, to sai dai Rasha ta musanta haka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.