An bukaci a haramta cin naman Kare da Mage a Switzerland
Kungiyar da ke yaki da cin zarafin dabbobi a Switzerland ta bukaci a hana al’ummar kasar kashe karnuka da mage suna cinyewa, sakamakon yadda yawancin al’ummar suka mayar da cin naman dabbobin abin marmari musanman a lokacin bukukuwa.
Wallafawa ranar:
Shugaban kungiyar da ke kare yancin dabbobi ya ce akalla kashi uku cikin dari na al’ummar kasar ne ke cin naman karnuka da mage a matsayin cimaka mai armashi, inda ya ce wasu ‘yan kasar na cin naman wadannan dabbobin gida ne a matsayin maganin sanyin kashi a lokacin bukukuwan kirsimeti.
Wannan ya sa yanzu kungiyar ta tashi tsaye wajen ganin an hana wadannan al’addu na cin zarafin wadannan dabbobi na gida a matsayin al’ada ko magani.
Wani dan siyasar kasar ya sheda wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa, babu abin da majalisa za ta yi, sai in har al’ummar kasar sun bayyana rashin amincewarsu, da wannan cin zarafi da ake yi wa Karnukan da mage a kasar ta Switzerland.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu