Isa ga babban shafi
Faransa

Jam'iyyar Socialists ta sha kashi a zaben kanan hukumomin Faransa

Jam’iyyar Socialists dake mulkin Faransa ta sha kashi a zabukan kananan hukumomin da aka yi jiya Lahadi. Wannan ya nuna yadda tsohon shugaban kasa Nicolas Sarkozy, da gamayyar jami’yyun ‘yan jari hujja suka sake kara karfi, kafin zaben shugaban kasa, da za a yi cikin shekarar 2017.Sakamakon zaben, da kamfanin dillacin labarum Faransa ya harhada, ya nuna gamayyar jami’iyun na ‘yan jari hujja, karkashin jagorancin jami’iyya UMP ta Nicolas Sarkozy sun sami gagarumar nasara ta kanan hukumopmin 66, daga cikin 101 da ake takara.Da alama Masu kada kuri’a sun huce haushin sun a gazawar gwamnatin shugaba Francois Hollande ta yan gurguzu, da ta gagara farfado da tattalin arzikin kasar dake ci gaba da durkushewa.Jami’iyyar ta Socialists ta tsira da kujerun kananan hukumomi 34 zuwa yanzu, yayin da ake ci gaba da jiran sakamakon karamar hukluma 1.Wannan sakamkon ya nuna cewa ‘yan Socialist din sun yi hasarar kujerun kanan hukumomin 25 da ‘yan jari hujja suka karbe, yayin da su kuma suka sami nasara lashe daya kawai daga daya bangare.Tsohon shugaban kasar Sarkozy ya shaida wa magoya bayan shi cewa jami’iyya tasu bata taba irin wannan babban kamu ba, inda ya kara da cewa jama’a sun nuna yadda suke adawa da matakan da gwamnati mai ci ke dauka. 

Tsohon shugaban Faransa, Nicolás Sarkozy
Tsohon shugaban Faransa, Nicolás Sarkozy REUTERS/Gonzalo Fuentes
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.