Harin bindiga ya kashe mutane 2 a kotun Milan
Wani mutun ya harbe alkali da lauya har lahira a harabar wata Kotu da ke birnin Milan na kasar italiya a lokacin da wata kotu ke tuhumar sa.
Wallafawa ranar:
Mutumin mai suna Claudio Giardiello na fusknatar tuhuma ne bisa basukan da suka yi masa katutu, kuma ya bindige alkali Fernando Ciampi da wani lauya mai suna Lorenzo Alberto bayan ya samu nasarar fisge bindiga, daga hannun wani jami’in tsaro da ke kai kawo a harabar kotun.
Bayan aikata laifin, Giardiello ya cika wandon sa da iska, sai dai tuni jami’an ‘yan sandan da suka bi sahunsa, inda suka kama shi a garin Virmercate da ke da nisan kilomita 25 daga birnin Milan.
An dai samu gawarwakin mutane uku a kotun, sai dai kuma rahotanni sun ce Giardiello na fama da matsalar bugun zuciya
Valerio Maraniello, wani lauya ne da ya taba tsayawa Giardiello, ya bayyana cewar, Girdiello mutun ne mai saurin Fushi, kuma ko da yaushe yana tunanin mutane cutar da shi za su yi, dan haka ba wani abin mamaki bane idan ya aikata haka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu