Isa ga babban shafi
Italiya

Za a rarraba ‘Yan ci-rani a sassan Turai

Kungiyar Tarayyar Turai na nazarin daukar matakin rarraba dubban ‘Yan ci-rani da suka tsallako ta kwale kwale a Italiya da Girka zuwa sassan kasashen Nahiyar. Kungiyar na ganin wannan matsala ce da ta shafi kasashen baki daya.

'Yan kasashen Afrika da suka bi ta Libya zuwa kasashen Turai domin  ci-rani
'Yan kasashen Afrika da suka bi ta Libya zuwa kasashen Turai domin ci-rani REUTERS/Hani Amara
Talla

A makon gobe ne mambobin Kungiyar Tarayyar Turai za su kada kuri’ar amincewa da daftarin.

‘Yan ci-rani kimanin 40,000 ne za a rarraba a sassan kasashen Turai, kuma a karshin tsarin, kungiyar za ta raba ‘Yan ci-ranin ta la’akari da girma da arzikin kasashen.

Dole sai daftarin ya samu rinjayen kuri’a daga mambobin kungiyar kafin amincewa da tsarin.

An dade dai kungiyoyin kare hakkin bil’adama na sukar kasashen Turai na rashin daukar matakan da suka dace na kula da rayukan ‘Yan ci-rani da ke mutuwa kusan a kullum a kokarinsu na tsallakowa zuwa Turai daga kasashen Afrika da Asiya.

Sai dai akwai yiyuwar kasashen Birtaniya da Denmark da Ireland za su kada kuri’ar kin amincewa saboda yadda suke da tsaurin ra’ayi game da bakin haure.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.