Girka na iya ficewa Turai-Lagarde
Hukumar Lamani ta duniya IMF tace akwai yiwuwar kasar Girka za ta fice daga jerin kasashen da ke amfani da kudin YURO, amma a cewar hukumar wannan ba zai zama dalilin rugujewar gamayyar kudin ba. Shugabar hukumar IMF Christine Lagarde da ke hira da manema labaru a kasar Jamus ta yi watsi da kalaman da hukumomin birnin Athens suka yi ne kan cewa suna tattaunawa da wadanda za su bai wa Girka bashi, don kawo karshen matsalolin da suka dabaibaye ta.
Wallafawa ranar:
Lagarde tace asusun na IMF ba zai ba Girka wani karin bashin ba, sai hukumomin kasar sun samar da sauye sauye ma su ma’ana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu