An nuna Bafaransa Isabelle da aka sace Yemen cikin faifan bidiyo
An fitar da faifan bidiyo da ke nuna wata Bafaransa mai suna Isabelle Prime wadda aka sace ranar 24 ga watan Fabarairun da ya gabata ita da mai yi ma ta tarjama a kasar Yemen.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta tabbatar da sahihancin wannan bidiyo, wanda ke nuna matar a cikin bakaken tufafi, sannan tana yin kira ga shugaban Faransa Francois Hollande da kuma takwaransa na Yemen Abd Rabbo Mansour Hadi da su taimaka domin ceto rayuwarta.
Mai magana da yawun ma’aikatar wajen Faransa Alexandre Giorgini, ya ce bincikensu ya tabbatar da cewa matar da ke magana ko shakka babu Isabelle ce.
Matar dai tana aiki ne a karkashin wani kamfanin ayyukan jinkai da ke birnin Sanaa fadar mulkin Yemen.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu