Isa ga babban shafi
Jamus

Masu zanga zanga sun yi barna a Jamus

Hukumomin kasar Jamus sun bayyana cewa daruruwan jama’a sun lalata gine gine ta hanyar jefe jefe a birnin Leipzig dake gabashin Kasar a lokacin wata zanga zanga

Tutocin kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya
Tutocin kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya 网络照片 DR
Talla

Ana ganin cewa, zanga zangar nada nasaba da taron G7 da manyan kasashen duniya masu karfin tattalin arziki za su gudanar a gobe lahadi.

Majiyar yan sandan Kasar ta ce, jami’an yan sanda uku ne suka samu raunuka sakamakon zanga zangar yayin da suka yi nasarar cafke mutun daya daga cikin masu boren.

Majiyar ta kara da cewa masu zanga zangar nata kona tayoyi a tsakiyar birnin na Leipzig. To sai dai tuni hukumomin Kasar suka fara gudanar da bincike domin gano hakikanin abinda ya tunzura jama’a har suka yi bore.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.