Isa ga babban shafi
Greece

Kasar Girka ta Gabatar da sabon Yarjejeniya ga kasashen Turai

PM Kasar Girka Alexis Tsipras ya gabata da wata sabuwar yarjejeniya ga shugabannin kasashen turai gameda dimbin bashin da ake bin kasar.

Fira Ministan Girka Alexis Tsipras tare da Shugaban Hukumar Kasashen Turai Jean-Claude Juncker
Fira Ministan Girka Alexis Tsipras tare da Shugaban Hukumar Kasashen Turai Jean-Claude Juncker Reuters/路透社
Talla

Majiyoyi na cewa Fira Ministan ya gabatar da sabuwar yarjejeniyar ce a tattaunawa ta wayan talho da yayi da shugannin Jamus Uwargida Angela Merkel da Shugaban Faransa Francois Hollande da kuma Shugaban kungiyar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker.

Kasar Girka yanzu haka tana fuskantar matsin lamba daga kasashen Turai da asusun bada lamuni na duniya domin ta sauke dimbin bashi da ake binta nan da ranar 30 ga wannan wata da muke ciki.

Muddin ta kasa sauke bashin yana iya zama sanadin ficewar ta daga kungiyar kasashen Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.