Isa ga babban shafi
Vatican

Fadar Vatican za ta gurfanar da daya daga cikin shugabanninta

Fadar Vatican ta sanar cewa za ta gurfanar da daya daga cikin tsoffin Shugabaninta a gaban kotu Jozef Wesolowski kan laifukan biyan kudi domin lalata da kananan yara da kuma daukan hoton bidiyon lalata wanda ya ajiye.

Jozef Wesolowski daya daga cikin Shugabanni a fadar Vatican
Jozef Wesolowski daya daga cikin Shugabanni a fadar Vatican REUTERS/Luis Gomez/Diario Libre/Files
Talla

Fadar ta ce ta dauki matakin ne bayan samun umarni daga shugaban darikar katolika ta duniya Paparoma Francis, domin ya zama darasi ga duk wani mai hallaya irin nasa a kokarin da take wajen samar da tsafta tsakanin malaman addini da ke aikata ba dai dai ba.

Gurfanar da Jozef Wesolowski za ta zama babbar shari’a wadda raban da ayi irinsa a fadar tun bayan gurfanar da Paolo Gabriel a shekarar ta 2012 kan laifukan sata da kwashe bayanan sirrin tsohon shugaban darikar Paparoma Benedict.

Tun a cikin watan satumban shekarar da ta gabata ne aka kama Jozef mai shekaru 66 a duniya, dan tsibirin Dominican, kuma shine mutum na farko da aka taba kamawa akan irin wannan laifin a Vatican.

A ranar 11 ga watan yulin wannan shekarar ake sa ran fara sauraran karar sa domin yanke masa hukunci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.