Isa ga babban shafi
Faransa-Saudi Arbia

Sarki Salman ya isa Tanger na Morocco

Ma’aikantan dake kula da bakin tekun kasar Faransa sun fara aikin mayar da wurin yawon bude idon yadda yake bayan Sarki Salman na Saudi Arabia ya katse hutun wata guda da ya shirya yi da tawagar sa mai dauke da mutane 1,000 inda ya tafi kasar Morocco.

Sarki Salman na Saudiya
Sarki Salman na Saudiya AFP PHOTO / STR
Talla

Sarki Salman ya bar gabar ruwan Cote d’Azur na kasar Faransa ne ranar lahadi,Cote d’Azur dake tashar jiragen saman Nice tare da mutane 500 zuwa Tangiers dake kasar Morocco.
Akalla mutane 150,000 suka sanya hannu kan takardar korafi kan yadda ziyarar Sarkin ta sa aka rufe gabar ruwan aka kuma jibge jami’an tsaro, a dai dai lokacin da Yan kasuwa ke maraba da shi saboda yadda suka dinga hada hadar kasuwancin su.
Rahotanni sun ce kowacce shekara bayan kamala azumin watan Ramadana attajirai da sarakunan kasahsen larabawa kan mamaye manyan otel otel dake Cannes dan hutu, abinda ya sa kungiyar masu otel din suka yi Allah wadai da korafin da mutane ke yi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.