Isa ga babban shafi
Faransa

Wani matashi ya kai hari cikin jirgin kasa a Faransa

Wani matashi dan asalin kasar Morocco  dauke da bindiga ya jikkata mutane biyu a cikin wani jirgin kasa daya taso daga Amsterdam zuwa birnin Paris na kasar Faransa bayan ya bude wuta a dai dai lokacin da Jirgin ke ganiyar gudu.

Jami'an Yan Sandan Faransa  sun cafke matashin da aka ce makamai ne suka cika jakarsa.
Jami'an Yan Sandan Faransa sun cafke matashin da aka ce makamai ne suka cika jakarsa. AFP/PHILIPPE HUGUEN
Talla

Mai Magana da yawun kamfanin jiragen kasa na Faransa ya ce wasu fasinjoji biyu 'yan Kasar Amurka ne suka ci karfin matashin kuma tuni ya shiga hannun jami’an tsaro.

To sai dai kawo yanzu, ba a gano dalillin da yasa dan bindijgan ya kai harin ba yayin da masu shigar da kara na Kasar ta Faransa suka ce, kwararru a fannin binciken ayyukan ta’addaci sun fara gudanar da bincike kan lamarin.

Ministan Harkokin cikin gida na Faransa Bernard Cazeneuve na kan hanyar sa ta zuwa yankin garin Arras a daidai inda lamarin ya auku.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.