'Yan awaren Catalonia sun yi nasara a zabe
‘Yan aware a Catalonia sun samu nasara a zaben da aka gudanar a jiya lahadi a yankin, lamarin da ke share fage ga yunkurinsu na ballewa daga kasar Spain.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A cikin daren jiya jagoran ‘yan awaren Artur Mas, ya bayyana wa taron gangamin magoya bayansa cewa sun yi nasara da akalla kashi 80 cikin dari na kuri’un da aka lissafa zuwa lokacin, abinda ke nuni da cewa kawancen jam’iyyun da ke goyon bayan ballewa daga Spain ne ya yi galaba.
Zabubbuka biyu ne aka gudanar a jiya a yankin na Catalonia mai yawan mutane milyan 7 da dubu dari biyar, na farko zaben ‘yan majalisa, na biyu kuwa na a matsayin kuri’ar jin ra’ayin jama’a ce game da ballewar yankin ko kuma ci gaba da kasancewa a cikin kasar Spain.
Firaministan Spain Mariano Rajoy, ya kasance daga cikin wadanda suka gudanar da yakin neman zaben kin amincewa da ballewar yankin na Catalonia, to sai dai rahotanni sun ce an samu fitowar jama’a fiye da kashi 7 cikin dari idan aka kwatanta da zaben da aka gudanar a 2012 a yankin.
Nasarar da ‘yan awaren suka samu dai na nuni da cewa mazauna yankin za su iya kada kuri’ar neman samun ‘yanci daga kasar Spain a shekara ta 2017
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu