Isa ga babban shafi
Faransa

‘Yan sanda na zanga-zanga a Faransa

Dubban ‘yan sanda Faransa ke gudanar da zanga-zanga saboda rashin kayan aiki da rashin ingantaccen tsarin shari’a, inda suka yi korafin cewa an yi watsi da su bayan bajintar da suka nuna yayin harin da aka kai kan birnin Paris cikin watan Janairu.

'Yan sanda Faransa dake zanga-zanga a Paris
'Yan sanda Faransa dake zanga-zanga a Paris REUTERS/Jacky Naegelen
Talla

Masu zanga zangar sun Fantsama a binin Paris da sauran manyan biranen kasar Faransa, inda suka sanya kananan riguna, suna masu furta kalaman cewa suna alfahari da kasancewar su ‘yan sanda, amma suna cike da takaicin watsin da gwamnati ta yi da su.

Wannan dai ita ce zanga zanga irinta ta farko a Faransa cikin shekaru 30, wacce ta dauko asali bayan musayen harbe harben da ‘yan sanda suka yi da wani mai laifi a makon jiya.

Harbe-harben, sun zo ne a dai-dai lokacin da jami’an tsaron kasar, ke zaman shirin ko-ta-kwana game da fargabar hare haren ta’addanci da ake fargabar kaddamarwa kan kasar.

To amma ana gani kamar zanga zangar ta yi tasiri, domin kuwa Firaministan kasar Manuel Valls, ya sanar da wasu sabbin matakan inganta aikin ‘yan sandan kasar.

Haka shima yayin taronsa na mako-mako da ministocin kasar, Shugaba Faransa Francois Hollande, ya jinjina wa jami’an ‘yan sandan tare da sauran jami’an tsaron kasar.

kana wani kakakin gwamnati Stephen Le Follande, ya ce a makon gobe ne ake sa ran shugaban kasar, zai gana da kungiyar jami’an ‘yan sandan kasar kan wannan batu.

Zanga zangar ‘yan sandan, ta haifar da matsala ga ministar shari’ar kasar Claudine Taubira, wadda ke ta kokarin kawo karshen yajin aikin lauyoyi a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.