Isa ga babban shafi
Faransa-Saudi Arabia

Faransa ta kulla kwangilar Euro biliyan 10 da Saudiya

Kasar Faransa ta sanar da cim ma wasu jerin yarjejeniya da suka kai na Euro biliyan 10 da kasar Saudi Arabia, yayin ziyarar da Firaminista Faransa Manuel Valls ya kai zuwa kasar ta Saudiya.

Firaministan Faransa  Manuel Valls da Ministan cikin gidan Saudia Mohammed bin Nayef bin Abdulaziz
Firaministan Faransa Manuel Valls da Ministan cikin gidan Saudia Mohammed bin Nayef bin Abdulaziz REUTERS/Saudi Press Agency
Talla

Yarjejeniyar sun hada da ta kwangiloli don inganta bangarorin tattalin arziki tare da habaka siyasar kasashen biyu.

Ofishin Firaministan, ya ce yarjejeniyar, ta shafi bunkasa makamashi, kiwon lafiya da kuma samar da abinci tsakanin kasashen.

Faransa dai, ta karkatar da hankali ne yanzu kan kyautata dangantaka da kasar ta Saudiyya duk da sukar da masu zazzafan ra’ayin kasar ke yi dangane da kaurin sunan da kasar ta larabawa ta yi kan batun ‘yancin bil’adama.

Yunkurin inganta dangantakar da Saudiyar ke yi da Faransa, wani bangare ne na kokarin fadada alakarta da kawayenta na asali irin su Amurka, domin kara mata karfin guiwar samun galaba a kan abokiyar kai ruwa ranarta a yankin, wato kasar Iran.

Rangadin kasashen Gabas ta Tsakiya ya kai Firaministan na Faransa kasashen Jordan da Masar .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.