Isa ga babban shafi
EU

EU na shirin tsawaita takunkumi a Rasha

Shugabanni kungiyar Kasashen Turai na shirin gudanar da wata Muhawara kan tsawaita takukunmi da aka kakabawa Rasha zuwa watanni 6 gaba, a wani taro da za su bude a wannan makon.

Ministar harkokin wajen Kungiyar Kasashen Turai Federica Mogherini
Ministar harkokin wajen Kungiyar Kasashen Turai Federica Mogherini REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Ministar harkokin wajen kungiyar Federica Mogherini ta ce daukan wannan mataki, ya biyo bayan kasa dai-daituwa zaman lafiya gabashin Ukraine.

Shugabanni kungiyar kasashen Turai 28 ne za su Gudanar da muhawara domin duba yiwuwar tsawaita takunkumin da aka kakabawa Rasha ko akasin haka.

Sanyawa Kasar Rasha takunkumi tattalin arziki,ya biyo bayan harbo jirgin saman Malaysia a watan Yuli shekarar 2014, wanda aka zargin ‘yan tawayen aware Ukraine dake samun goyon bayan Rasha.

A kallamanta bayan ganawa da ministocin Turai, Federica Mogherin tace sau da dama ana karya yarjejeniya zaman lafiya da aka cimma a birnin Minsk,  don haka basa tunani dage wa Rasha takunkumi a yanzu.

Taron kungiyar da za a fara ranar alhamis na tsawon kwananki biyu, zai mayar da hankali kan wanna batu ne domin bijiro da matakan daya kamata a dauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.