An abkawa Musulmi a Masallaci a Faransa
Wasu gungun masu zanga-zanga a Faransa sun abkawa wani masallaci tare da Kona Al Qur’ani mai tsalki a yankin Ajaccio. Lamarin ya faru ne da yammacin jiya Juma’a bayan an kashe wasu ‘Yan Sanda da jami’an kashe gobara guda biyu a yankin Jardins de L'Empereur.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Mutane sama da 150 suka hada gangami domin nuna goyon baya ga ‘Yan sanda bayan kashe jami’ansu guda biyu.
Amma daga baya kuma wasu daga cikin masu zanga-zangar suka abkawa Masallaci suna fadin Larabawa su fice kasarsu tare da farfasa kofa da tagogin masallacin da kuma kona wani sashe na Al Qur’ani mai tsarki.
Gwamnatin Faransa dai ta yi allawadai da al’amarin wanda ta danganta a matsayin nuna wariya da kyamar baki.
Jam’iyyar ‘Yan kishin kasa ce ta Marine Le Pen mai adawa da bakin haure ta lashe zaben kananan hukumomi da aka gudanar a yankin Corsica inda aka kai wa musulmin harin a jiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu