Isa ga babban shafi
Faransa

Ministar Shari’ar Faransa ta yi murabus

Ministan shari’ar kasar Faransa Christiane Taubira ta yi murabus a yau Laraba kan adawa da manufofin gwamnati na kwace takardun ‘Yan kasa da aka samu suna da alaka da ayyukan ta’addanci.

Christiane Taubira, Ministar shari'ar Faransa mai murabus
Christiane Taubira, Ministar shari'ar Faransa mai murabus REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Ministan ta yanke shawarar yin murabus ne duk da tana cikin manyan jiga jigan jam’iyyar gurguzu ta shugaba François Hollande.

Tun Bayan harin Paris da aka kai a ranar 13 ga watan Nuwamba inda mutane 130 suka mutu, gwamnatin Hollande ta bukaci kafa dokar kwace takardun ‘yan kasa da aka samu suna da alaka da ayyukan ta’addanci.

Tun lokacin ne Minsitan shari’ar kasar Christiana Toubira ke adawa da matakin.

Christiane Toubira dai bakar fata ce da ke rike da mukamin babbam minista a Faransa tun a 2012.

Wannan ne kuma ya haifar da sabanin ra’ayi tsakaninta da Shugaba Francios Hollande da Firaministansa Manuel Valls.

Faransa dai na son tabbatar da dokar ne karkashin sabbin matakan tsaron da kasar ke dauka na tsaro domin dakile barazanar hare haren ta’addanci, a yayin ake ci gaba da samun Faransawa wadanda ba ‘yan asalin kasar ba da ke da alaka da mayakan IS masu da’awar jihadi.

A yau Laraba ne Firaministan kasar ya gabatar daftarin dokar a gaban majalisa kafin soma muhara kan batun a watan Fabrairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.