Isa ga babban shafi
Cuba

Raul Castro na Cuba ya kai ziyara a Faransa

Shugaban kasar Cuba Raul Castro ya fara ziyarar aiki a Faransa a yau Litinin, ziyararsa ta farko a kasashen Turai da ake ganin wani mataki na farfado da hulda tsakanin kasar kuma da kasashen yammaci.

Shugaban Cuba Raul Castro tare da Shugaban Faransa Francois Hollande
Shugaban Cuba Raul Castro tare da Shugaban Faransa Francois Hollande AFP/ADALBERTO ROQUE
Talla

Raul Castro mai shekaru 84 wannan ce ziyararsa ta farko a Turai tun lokacin da ya gaji yayansa Fidel Castro a 2006.

Tun a ranar Assabar ne shugaban ya isa Faransa, kuma wannan na zuwa ne bayan Cuba ta sasanta da Amurka da suka dade suna gaba da juna.

A lokacin da ya ke karbar bakuncin shi, Shugaban Faransa Francois Hollande ya danganta ziyarar a matsayin wani mataki na inganta hulda tsakaninsu da Cuba.

Ana sa ran Shugaba Castro zai sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyin kasuwanci tsakanin Cuba da Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.