Isa ga babban shafi
Faransa

Yaran makaranta sun rasu a hadarin mota a Faransa

Akalla kananan yaran makaranta shida ne suka rasa rayukansu bayan motar da ke dauke da su ta yi taho mu gama da wata babbar motar dakon kaya a kudancin Faransa a yau Alhamis.

Motar daukan dalibai da ta yi hadari a Faransa
Motar daukan dalibai da ta yi hadari a Faransa XAVIER LEOTY / AFP
Talla

Wannan na zuwa ne kwana guda bayan aukuwar wani hadarin mota da ya shafi motar daukan daliban makaranta, inda yara biyu suka rasu.

Hadarin yau ya auku ne da misalin karfe 7 na safe agogon kasar a yankin Rochefort yayin da rahotanni ke cewa katuwar motar ta yi dakon buraguzan duwatsu ne.

Ita kuwa motar daliban na dauke da jumullar yara 17 ne yayin da uku daga cikin su suka samu rauni kamar yadda jami’an 'yan sanda suka tabbatar.

Tuni dai shugaban kasar Francois Hollannde ya aike da sakon ta’aziyar ga iyalan mamatan tare da yin alkawarin gudanar da bincike domin gano musabbabin aukuwar lamarin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.