Isa ga babban shafi
Girka-Turai

Macedonia ta hana yan gudun hijira shiga kasar

Dubban yan gudun hijirar da suka fito daga Afghanistan ne suka makale akan iyakar kasar Girka bayan kasar Macedonia ta rufe iyakokin ta, al’amarin dake ci gaba da tayar da hankulan mayan kasashen Duniya.

Yan gudun Hijira a kan hanyar su ta zuwa kasar Macedonia
Yan gudun Hijira a kan hanyar su ta zuwa kasar Macedonia REUTERS/Ognen Teofilovski
Talla

Bayanai sun ce baki 8,000 matsalar ta ritsa da su a gabar ruwan Piraeus bayan Macedonia ta kaddamar dakile kwararan bakin.
Daruruwan yara kanana dauke da allunan dake rokon cewar a taimaka masu ketara iyakar sun yi dafifi a gabar ruwan.
Hukumomin Macedonia sun dau wannan mataki ne bayan da kasashen Serbia da Slovenia suka takaita adadin yan gudun hijira da zasu shiga kasashen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.