Isa ga babban shafi
Rasha

Rasha ta soma janye dakarunta daga Syria

A yau talata ne dakarun kasar Rasha dake taimakawa shugaba Bashar Al-assad na Syria yakar ‘yan ta’adda suka soma janyewa daga kasar bisa umarnin shugaba Vladimir Putin

Shugaban kasar Syria  Bashar Al-Assad da na Rasha Vladimir Putin
Shugaban kasar Syria Bashar Al-Assad da na Rasha Vladimir Putin REUTERS/Alexei Druzhinin/RIA Novosti/Kremlin
Talla

A daren jiya ne shugaba Vladimir Putin ya sanar da bukatar kasarsa na janye dakarunta daga Syria, kamar yadda dai aka ji labarin shiga yakin kwatsam a farko haka aka ji labarin janyewarta daga Syria, bayan watanni 4 da Rasha ta kwashe tana luguden wuta akan mayakan jihadi da suka hana zaman lafiya a Syria

Mr Putin wanda ya sanar da matakin janye dakarun yace hakan shine daidai ganin haka ta cimma ruwa a kokarin Rasha na tarwatsa kungiyoyin ‘yan ta’dda

Yanzu haka ma dai tawagar Majalisar Dinkin Duniya da bangarorin dake rikici da juna a Syria sun koma zaman tattauna hanyoyi kawo karshen rikicin na Syria a birnin Geneva

Shekaru sama da 4 aka kwashe ana fama da tashe tashen hankula kuma mutane sama da 300,000 ne suka rasa rayukansu baya ga miliyoyi da suka tsere daga muhallinsu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.