Isa ga babban shafi
Faransa

Attajiri Serge Dassault zai sake gurfana a gaban kotu

 Shaharren attajirin Serge Dassault zai sake gurfana gaban kotu bisa laifin hannu a cuwa-cuwar kudadden haraji na miliyoyin Euro da kuma laifin kasa bayyana kaddarorin da ya mallaka ga hukumomin kasar Faransa

Attajiri Serge Dassault
Attajiri Serge Dassault AFP PHOTO/JACQUES DEMARTHON
Talla

kamar yadda rahotanni a Faransa ke cewa attajiri Serge Dassault zai amsa tambayoyi akan wasu miliyoyin kudadde da ake zargin shi da boyewa a kasar Luxemborg da kuma Liechstenstein

Dassault wanda ke mataki na 4 a masu kudin Faransa zai kuma fuskanci shari’a bisa zargin hannu a badakalar siyan kuri’u a garin Corbeil dake birnin Paris a lokacin da yake magajin garin.

Attajirin mai shekaru 90 mamba ne a Majalisar dokokin kasar, nan ma akwai batun fuskantar shari’a bisa kasa bayyana kaddarorin da ya mallaka ga hukumomin kasar ta Faransa.

A watan nuwambar shekarar 2014 lokacin da aka soma yunkurin tuhumar attajirin da hannu a cuwa-cuwar kudadde, daya daga cikin akantar Dassault ya shedawa masu bincike a Faransa cewar ya taba kaiwa Dassault kudi yuro miliyan 53 a jakar leda sai dai kuma Dassault ya musanta zancen karba kudadden baki daya

An dai tsayar da ranar 4 ga watan Yuli a matsayin ranar da za’a soma sauraren karraraki da ake zargin Serge Dassault a gaban shari’ar
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.