Isa ga babban shafi
Faransa

Shugaba Hollande ya amsa tambayoyin manema labarai

Farin jinin shugaban Faransa Francois Hollande na ci gaba da raguwa a tsakanin al’ummar kasar, yawan ‘yan kasar da suka ware lokacinsu domin sauraran zantawar shugaban da ‘yan jarida a jiya bai taka kara ya karya ba.

Francois Hollande Shugaban kasar Faransa a tattaunawa da manema labaren Canal France 2
Francois Hollande Shugaban kasar Faransa a tattaunawa da manema labaren Canal France 2
Talla

Shugaba kasar ta Faransa Francois Hollande dake ta kokarin sake dawo da martabar sa a jiya alhamis ya bayyana a tashar talabijen na Canal France 2 na kasar domin amsa tambayoyin manema labarai.

Idan aka yi la’akari da yadda Faransawa ke kallon tattaunar da shugabanninsu ke yi musamman akan batutuwan da suka shafi siyasar kasar kalilan ne suka mayar da hankali zuwa wanan tattaunawa.
Yayi da rage shekara daya a gudanar da babban zaben kasar Faransa ,Francois Hollande shugaban kasar na sa ran gani yan kasar sun bashi goyan bayan da ya dace domin sake samun wani sabon wa'adi na biyu a babban zabe  na shekara ta 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.