Trump bai cancanci jagorantar Amurka ba-Obama
Shugaban kasar Amurka Barrack Obama ya bayyana dan takarar neman shugabancin kasar karkashin jam`iyyar adawa ta Republican Donald Trump a matsayi wanda bai cancanci shugabancin kasar ba.
Wallafawa ranar:
Obama ya ce yana mamakin yadda har yanzu j`iyyar Republican ke marawa Trump din baya a takarar tasa ta neman shugabancin kasar.
Shugaban kasar Amurkan ya ce duk da a baya ya samu banbancin manufofi tsakaninsa da yan takarar Jam`iyyar Republican, bai taba daukarsu a matsayin wadanda zasu gaza wajen jagoranci ba.
Donald Trump na shan suka bisa batanci ga wasu daga cikin iyayen sojin Amurka da suka mutu a fagen fama, sai kuma goyon bayansa da ya nuna ga kasar Rasha bisa manufarta kan yankin Crimea.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu