Isa ga babban shafi
Faransa

An tsare mutane 7 saboda yunkurin hari a Faransa

Hukumomin Faransa sun tsare mutane bakwai bayan jami’an tsaro sun yi nasarar dakile yunkurin kaddamar da wani hari a birnin Paris.

Jami'an tsaron Faransa na bincike kan yunkurin kai harin na ta'addanci
Jami'an tsaron Faransa na bincike kan yunkurin kai harin na ta'addanci REUTERS/Christian Hartmann
Talla

Ana zargin mutanen na da alaka da kungiyar IS mai ikirarin jihadi a Syria kamar yadda mai shigar da kara na kasar, Francois Mollins ya bayyana.

Shugaban kasar, Francois Hollande ya ce, an yi nasarar wargaza yunkurin harin na ta’adannaci, wanda aka shirya kai wa da wata mota makare da tukwanen iskar gas.

Akwai mata guda uku da jami’an tsaron suka kama saboda zargin cewa, kungiyar IS na kokarin shigar da su cikin mambobinta.

Rahotanni sun ce, daya daga cikin matan ta ayyana mubaya'arta ga kungiyar IS a cikin wata wasika da jami’an tsaron suka samu.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai, aka ajiye motar a kusa da majami’ar Notre Dame da ke Paris, in da aka samu tukwanen gas guda biyar da gajeruwar tabar sigari har ma da kwalaben man diesel guda uku a cikinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.