Hungray
Luxembourg ta bukaci korar kasar Hungary daga Tarayyar Turai
Ministan harkokin waje na kasa Luxembourg Jean Asselborn, ya bukaci kungiyar tarayyar turai EU ta kori kasar Hungary daga cikinta.
Wallafawa ranar:
Talla
Asselborn ya ce kiran yazama dole idan akayi la’akari da yawaitar sabawa dokokin tarayyar turan da kasar ta Hungary ke yi.
Asselborn ya ce saba ka’idojin sun kunshi, wulakanta masu gudun hijira, tauye bangaren Shari’ah na kasar da kuma rashin bawa kafafen yada labarai cikakken ‘yanci.
Sai dai kuma Ministan Harkokin wajen na Hungary Peter Szijjarto ya maida martanin cewa, kiran suka ne kawai marar ma’ana ake yi ga kasarsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu