Isa ga babban shafi
Birtaniya

'Yan adawa suna yunkurin hana ficewar Birtaniya daga Turai

Yan Majalisa daga jam’iyyar adawa a Birtaniya, sun ce ba zasu goyi bayan ficewar kasar daga tarayyar Turai ba, har sai gwamnati ta sake bawa al’ummar kasar damar kada kuri’ar raba gardama karo na biyu kan bukatar.

Firaministan Birtaniya Theresa May
Firaministan Birtaniya Theresa May REUTERS/Kirsty Wigglesworth/pool
Talla

Da fari Firaministan Birtaniya Theresa May ta bukaci fara tattaunawar karshe kan ficewar kasar daga EU a ranar 31 ga watan Mayu na Sabuwar shekara, to sai dai wata babbar kotu a kasar ta ce dole Majalisar Birtaniyar ta kada kuri’a kan bukatar.

Wani jagora a Liberal Democrat Tim Farron, ya ce, tuni wasu ‘yan majalisar Birtaniya da ke goyon bayan zaman kasar a Tarayyar Turai, suka fara shirin yadda zasu yi watsi da batun ficewar kasar daga EU, idan aka gabatar da bukatar gaban Majalisa.

Sai dai a martaninsa, Ministan da ke shugabantar Shirin ficewar Birtaniya daga EU, David Jones ya zargi ‘yan adawa da yunkurin murde, zabin jama’ar kasar, na son ficewa daga tarayyar turai a ranar 23 ga watan Yuni da ya gabata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.