Isa ga babban shafi
Faransa

Hazon da ya mamaye birnin Paris zai ragu

A karshen wannan makon ne, birnin Paris da kewayensa zai fita daga cikin gurbatacen yanayi na hazo mai yawa da ya shafi babban birnin kasar ta Faransa a cikin kwanaki 10 da suka gabata, kamar yadda hukumar dake zura ido kan yanayi ta sanar 

kura da hazon da suka mamaye birnin  Paris
kura da hazon da suka mamaye birnin Paris REUTERS/Christian Hartmann
Talla

Amélie Fritz, ta hukumar dake lura da kyawon yanayi a kasar ta Faransa Airparif. ta sanar da kamfanin dilancin labaren Faransa na AFP cewa, kura da hazon da suka mamaye birnin na Paris zasu ragu a karshen mako, haka shi ma cinkoson ababen hawan, domin ana zaton samun tashin iskan da zai watsa hazon da ya yi saura a sararin samaniyar birnin

To amma doli ne a yi taka tsantsan dangane da yadda yanayin zai iya kasancewa a makon gobe bisa halin da yanayin zai samu kansa inji hukumar da ta kara da cewa, babu wani tabbacin idan har yanayin zai inganta a mako mai zuwa

Yau da mako guda yankin birnin paris a dushe yake sakamakon bayyanar giza gizan kura, al’amarin da yasa mahukumtan birnin takaita zirga zirgar ababen hawa.

Yankin Rhône, mai kumshe da masana’antu da Normandie dake yammaci hade da yankunan arewacin faransa, da garuruwan dake yankunan tsaunuka Alpes ko Pyrénées, duk suna fuskantar gurbacewar iskar sakamakon hudowar sanyin hunturu a kasar .

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.