Isa ga babban shafi
Syria

An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Syria

Kasashen Rasha da Turkiya sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Syria, dokar za ta fara aiki a daren yau Laraba, domin bada damar kai agaji ga fararren hula da kuma kwashe su daga yankunan ‘yan tawaye.

Kasashen Rasha da Turkiya sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Syria.
Kasashen Rasha da Turkiya sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a Syria. Ảnh : REUTERS/Maxim Shemetov
Talla

A satin da ya gabata ne dai Rasha, Iran, da kuma Turkiya suka sanar da cimma matsayar aiwatar da tsagaita wutar bayan taron da wakilan kasashen suka gudanar a birnin Moscow, ba tare da sanya wakilan Amurka ba.

Kamar yarjejeniyoyin da suka gabata, tsagaita wutar ba ta shafi kugiyoyin ‘yan ta’adda ba irinsu ISIL a kasar ta Syria.

To sai dai fa, Ministan harkokin waje na Turkiya Mevlut Cavusoglu, ya yi Karin bayanin cewa, yarjejeniyar na kunshe da daftari biyu daya kan batun yarjejeniyar tsagaita wutar, yayin da dayan kuma kan warware takaddamar da ke tsakanin gwamnatin shugaba Bashar Al-assad da ‘yan adawar kasar, wadda za’a yi a Astana, babban birnin kasar Kazakhstan. Amma kafin nan da gobe Alhamis za’a tattauna batun tsagaita wutar tsakanin ‘yan tawayen da jami’an Rasha a birnin Ankara na Turkiya.

To sai dai kuma bangaren ‘yan adawar Syria, sun ce batun tsagaita wuta kawai suka sani ban da batun tattaunawar sulhu tsakaninsu da gwamnati.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.