Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai

An tsawaita dokar tsaro a iyakokin Turai

Hukumar Tarayyar Turai ta sanar ta tsawaita takaita amfani da takardun izinin zirga-zirga cikin kasashen a karin watanni uku domin warware matsalolin bakin haure da suka addabe ta.

Turai ta dauki matakan rage kwararar bakin haure da 'yan gudun hijira
Turai ta dauki matakan rage kwararar bakin haure da 'yan gudun hijira REUTERS
Talla

Kasashen Austria da Jamus da Denmark da Sweden da Norway ne suka fara sa idanu na shekara ta 2015 a lokacin da aka sami matsalar bakin haure da ‘yan gudun hijira musamman daga kasar Syria da Gabas ta Tsakiya da kasashen Afrika.

Mataimakin Shugaban Hukumar Tarayyar Turai Frans Timmermans ya fadi cikin wata sanarwa cewa an yi nisa wajen dage haramcin matakan takaita shiga kasashen juna amma kuma akwai sauran wasu gyare-gyare da za a yi.

A cewarsa ya dace a bar kasashen da ke cikin kungiyar su ci gaba da tsarin da suke bi yanzu haka na tsawon watanni uku.

Kungiyar Tarayyar Turai da farko ta ce za a maido da aiki sosai da tsarin hana takunkumin zirga-zirga tsakanin kasashen juna da suka kunshi kasashen 22 da Norway da Iceland da Switzerland ya zuwa karshen shekarar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.