Isa ga babban shafi
Rasha

Kotu ta haramtawa Navalny shiga siyasar Rasha

Wata kotu a Rasha ta yanke hukuncin dakatar da Madugun `yan adawar kasar, Alexeī Navalny daga shiga harkokin siyasa na tsawon shekaru 5.

Jagoran `yan adawa a Rasha Alexeï Navalny.
Jagoran `yan adawa a Rasha Alexeï Navalny. REUTERS/Maxim Shemetov
Talla

Hukuncin ya biyo bayan samun Navalny da laifin barnatar da wasu makudden kudadde daga cikin kasafin kudin gwamnatin lardin Kirov, yayin wata cinikayyar gumaguman iccen timber da ya jagoranta a shekarun baya, a lokacin da ya rike mukamin mai bawa gwamnatin lardin shawara na musamman.

Hukuncin kotun dai ya tsayawa ne kan haramcin kawai ba tare da iza keyar sa zuwa kurkuku ba.

Ana dai zaton hukuncin ya dakile aniyar Navalny, ta tsayawa takara a zaben shugabancin kasar da za`a yi a shekarar 2018, ganin cewa dokokin Rasha sun haramtawa wanda ke karkashin hukuncin kotu ya rike mukamin siyasa.

To sai dai a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Internet, Navalny ya ce yana nan daram kan aniyarsa ta tsayawa takarar neman shugabancin kasar.

Masharhanta dai na ganin Navalny na da wannan kwarin gwiwa saboda a gefe guda, kundin tsarin mulkin Rasha ya bawa wanda baya tsare a gidan kurkuku damar shiga siyasa, abinda yasa lokaci ne kawai zai nuna yadda zata kaya.

A 2013 kotun da ke Kirov ta dakatar da Navalny daga rike mukaman siyasa tsawon shekaru 5, wanda daga baya wata kotun tarayyar turai ta soke hukuncin a watan Fabarairu na shekarar 2016.

To sai dai kuma a watan Nuwamba a dai shekarar ta 2016, kotun kolin Rasha, ta bada umarnin a sake sauraron shari`ar bisa zargin da aka yiwa Navalny, abinda ya bayyana da bita da kullin siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.