Isa ga babban shafi
Britaniya

Ficewar Birtaniya a Tarayyar Turai ba alheri ba ne- Blair

Tsohon Firaiministan Birtaniya Tony Blair ya yi kira ga ‘yan kasar da su tashi tsaye tare da canza tunani akan ficewar kasar daga kungiyar Tarayyar Turai.

Tsohon Firaiministan Britaniya Tony Blair ya ce ficewar kasar daga EU ba alheri ba ne.
Tsohon Firaiministan Britaniya Tony Blair ya ce ficewar kasar daga EU ba alheri ba ne. Reuters / Pascal Lauener
Talla

Mista Blair ya ce kuri’ar raba gardama da ta amince da ficewa kungiyar Tarayyar Turai barazana ne ga Birtaniya.

Wannan ne karon farko da Tony Blair ya yi tsokaci akan ficewar Birtaniya daga EU.

A cewar Mista Blair mutane sun kada kuri’ar raba gardama ne a jahilce ba tare da sun fahimci manufofin ficewar ba.

Tsohon Firaministan ya ce mutanen Birtaniya yanzu na da ‘yancin su sauya ra’ayinsu, kamar yadda ya ke shaidawa wani taron masu ra’ayin Tarayyar Turai a Birtaniya.

A cikin jawabinsa Blair ya ce yanzu hakkinsu ne a matsayinsu na shugabanni su wayar da kan mutanen Birtaniya su sauya ra’ayinsu..

Ya ce yanzu lokaci ne na kare abinda suka yi imani da shi.

Firaiminista Theresa May ta sha alwashin tabbbatar da ficewar Birtaniya a watan gobe karkashin ayar doka ta 50 ta Tarayyar turai.

Amma Blair ya soki May da mambobin gwamnatinta ta yadda matsin lambar siyasa zai sa su amince Birtaniya ta fice duk da ba su goyi bayan ficewar ba a zaben raba gardama.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.