Isa ga babban shafi
Holland

Wilders ya sha kaye a zaben kasar Holland

Firaministan kasar Holland, Mark Rutte ya samu nasarar zarcewa bisa kujerarsa, bayan jam’iyyarsa ta Liberal, mai sassaucin ra’ayi, ta samu nasara kan jam’iyyar PVV masu kishin kasa da Geert Wilders ke wa takara a zabukan kasar da aka yi a Larabar da ta gabata.

Firaministan kasar Holland Mark Rutte na jam'iyyar VVD da ya samu nasarar zarcewa bisa mukaminsa.
Firaministan kasar Holland Mark Rutte na jam'iyyar VVD da ya samu nasarar zarcewa bisa mukaminsa. REUTERS/Michael Kooren
Talla

An dai kwashe makwanni Geert Wilders yana matsayi na farko a kuri’ar jin ra’ayin jama’a, saboda manufofinsa na kyamar addinin Islama, da alkawarin rufe Masallatai, sai kuma hana karanta Al Qur’ani mai girma, amma sakamakon zaben ya tabbatar da nasarar jam’iyyar Firaministan Rutte, da ta samu kujeru 32 a majalisa yayin da Wilders ya samu kujeru 19.

A shekaru 20 da ya kwashe yana siyasa, Wilders yayi ta fama da yaudarar kuri’ar jin ra’ayin jama’a, wadda ke nuna masa fari kafin zabe, amma da zarar an gudanar da zaben sai yaga baki, kamar dai yadda wannan sakamakon zaben ya nuna.

Kimanin ‘yan kasar Holland miliyan 12 da rabi ne sukai fitar dango zuwa rumfunan zabe don kada kuri’unsu, a zaben da jam’iyyun kasar 28 suka fafatawa domin dare kujeru 150 na majalisar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.