Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai

EU na bikin cika shekaru 60 da kafuwa

A yayin da suke gudanar da bikin cika shekaru 60 da kafa kungiyar Tarayyar Turai a wannan Asabar a birnin Rome, shugabannin nahiyar za su sabanta yarjejeniyar da aka kafa nahiyar akai.

Lokacin da kasashen Turai guda shida suka sanya hannu don assasa kungiyar Tarayyar Turai a birnin Rome a ranar 25 ga watan Maris na shekarar 1957
Lokacin da kasashen Turai guda shida suka sanya hannu don assasa kungiyar Tarayyar Turai a birnin Rome a ranar 25 ga watan Maris na shekarar 1957 © AFP/Archives
Talla

Shugabannin dai na ganawa ne a birnin Rome, in da kasashen Turai guda shida suka fara assasa Kungiyar Tarayyar a ranar 25 ga watan Maris na shekarar 1957.

Sai dai taron na wannan lokacin na gudana ne ba tare da Birtaniya ba da ta kada kuri’ar ficewa daga Turai.

Shugaban mabiya Darikar Katolika ta Duniya, Fafaroma Francis zai gabatar da jawabi ga shugabannin, bayan ya gargadi cewa nahiyar na fuskantar barazanar wargajewa.
 

Fadar shugaban Amurka ta White House ta aika da sakon taya murnar cika shekaru 60 ga shugabannin Tarayyar Turai, yayin da aka kirge matakan tsaro a birnin na Rome, musamman ganin harin ta'addanci na baya-bayan nan da aka kai Birtaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.