Isa ga babban shafi
Faransa

Kusan kashi 70 na al'ummar Faransa sun kada kuri'unsu

Zaben shugabancin Faransa ya gudana a karkashin dokar ta baci da hukumomin kasar suka ayyana saboda fusknatar barazanar tsaro.

Wasu daga cikin 'yan kasar Faransa yayin layin Jefa kuri'unsu a zaben shugabancin kasar.
Wasu daga cikin 'yan kasar Faransa yayin layin Jefa kuri'unsu a zaben shugabancin kasar. REUTERS/Luke MacGregor
Talla

A karo na farko kenan a shekarun baya-bayan nan da Faransawa ke kada kuri’u a karkashin dokar ta ta baci a tarihin kasar.

Da misalin karfe takwas na safiyar yau agogon Faransa ne aka bude rumfunan zaben a dukkanin fadin kasar, yayin da kasashen duniya ke ci gaba da sanya ido kan yadda zaben ke gudana.

Kimanin mutane miliyan 46. 87 ne suka yi rijistar kada kuri’unsu a rumfunan zabe dubu 66 da 546, inda kuma aka girke dubban jami’an tsaro don bai wa jama’a kariya.
Tsauraran matakan tsaro a zaben na zuwa ne bayan wani mutun ya kai harin ta’addanci a kasaitacciyar unguwar Champs Elysee a ranar Alhamis da ta gabata, in da ya kashe dan sanda guda tare da jikkata mutane uku.

Ma’aikatar cikin gidan Faransa ta ce, zuwa yammacin ranar Lahadi, an samu kusan kashi 69.42 na jama’a da suka fito, don kada kuri’unsu, adadin da ya kusan kamo wanda aka samu a zagayen farko na zaben kasar na shekarar 2012, in da a wancan lokaci aka samu kashi 70. 59.

Wata kuri’ar jin ra’yin jama’a ta nuna cewa, Marine Le Pen ta jam’iyyar National Front da Emmannel Macron mai zaman kansa da Francois Fillon mai matsakaicin ra’ayi da kuma Jean Luc Malenchon mai ra’ayin rikau na kan gaba a zaben na yau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.