Isa ga babban shafi
Faransa

Sakamakon zaben 'yan majalisu haske ne ga Macron

Jam’iyyar shugaban Faransa Emmanuel Macron, Le Republic en Marche, ta samu gagarumin rinjaye a zaben ‘yan majalisu, masu wakiltar Faransawa da ke zaune a kasashen ketare da ya gudana.

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron. REUTERS/Charles Platiau
Talla

Sakamakon zaben, ya nuna cewa, “en Marche” ta lashe kujeru 10, daga cikin 11 da ke wakilcin Faransawan, mazauna kasashen waje.

A mafi akasarin mazabu goman da ‘yan takarar Emmanuel Macron suka samu nasarar, sun lashe sama da kashi 50 na kuri’un da aka kada, to amma duk da haka, dole a sake fafatawa a zagaye na biyu kafin tabbatuwar nasarar da suka samu, kasancewar basu samu yawan kuri’un da ake bukata ba.

Ko da ya ke kuri’un wadannan mazabu 11 da ke wakiltar faransawa mazauna waje, ba wai suna wakiltar ainahin ra’ayin al’ummar kasar bane, manazarta sun tabbatar da cewa, nasarar ta kara karfafa hasashen da aka yi cewar Jam’iyyar ta Emmanuel Macron zata samu gagarumin rinjaye a zaben ‘yan majalisun kasar da za’a yi a ranar 11 ga watan Yuni.

Sakamakon wata kuri’ar jin ra’ayi da aka gudanar a shekaranjiya, ya nuna cewa Jam’iyyar Le Republic en Marche, zata lashe kashi 29.5 na kuri’un da za’a kada, a zaben ‘yan majalisun kasar zagaye na farko da za'a yi a ranar 11 ga watan da muke ciki.

Hasashen ya kara da cewa jam’iyyar adawa ta Republican, zata samu kashi 23, daga cikin kuri’un, National Front ta Marine Le Pen, zata samu kashi 17, yayinda Socialist ta tsohon shugaban kasa Francios Hollande, zata lashe kashi 8.5.

A zagaye na biyu na zaben ‘yan majalisun kuwa, sakamakon kuri'ar jin ra’ayin ya nuna cewa, jam’iyyar Le Republic en Marche ta Macron, ka iya lashe 385 zuwa 415 daga cikin kujerun ‘yan majalisun kasar 577 da ke akwai.

Macron dai na bukatar samun wannan rinjaye domin cimma burinsa na aiwatar da manyan manufofin gwamnatinsa, da suka hada da yiwa dokokin kwadagon kasar garambawul, da kuma samar da euro biliyan 50, da za’a zuba a fannin inganta makamashi da samar da ayyukanyi.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.