Rasha
Rasha ta daure Navalny kwanaki 30
Wata Kotun Rasha ta daure shugaban 'yan adawar kasar Alexie Navalny kwanaki 30 a gidan yari saboda samun sa da laifin shirya zanga- zangar adawa da gwamnati ba tare da izini ba.
Wallafawa ranar:
Talla
Zanga-zangar ta jiya Litinin ita ce ta biyu mafi girma da Navalny ya kira a fadin Rasha domin adawa da gwamnatin kasar da ake zargi da laifukan cin hanci da rashawa.
Rahotanni sun ce, akalla mutane 1,500 'Yan Sanda suka kama lokacin gudanar da zanga-zangar.
Kasar Amurka ta bukaci gaggauta sakin wadanda aka kama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu